✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ce ta 3 a kasashen da suka fi cin naman kare a duniya —Bincike

A watan Yulin bara Shugaba Buhari ya haramta cin naman karen da kuma sayar da shi.

Wani binciken masana ya bayyana cewar Najeriya ce kasa ta 3 da aka fi cin naman kare a duniya, bayan kasashen Koriya ta Kudu da Vietnam.

Rahotan binciken da Mathew Nash ya jagoranta wanda Jaridar Premium Times ta wallafa yayi karin haske akan kasashen da kiwon karnuka ke da tasiri da akasin haka a wannan shekara ta 2022.

Rahotan ya ce duk da ya ke ana matukar cin naman karan lokacin bukukuwa a China, kasar bata cikin jerin kasashe 3 na duniya da aka fi cin naman karan kamar yadda binciken da aka gudanar a kasashe 51 ya nuna.

Wannan binciken ya mayar da hankali ne akan kasashen da ake kare hakkin karnukan da kasashen da ake barin karnukan su shiga otel-otel da wadanda ke da isassun likitocin dake kula da su da masu kungiyoyin kare hakin dabbobi da masu fama da barazanar kamuwa da cutar cizon karnukan da kuma wadanda ke da dokar alaka tsakanin dabbobi da mutane.

Najeriya ta zo ta 45 daga kasashe 51 da suka cika mizanin binciken da aka gudanar da maki 44.41, yayin da Italiya ke matsayi na farko sai New Zealand sannan Faransa da Birtaniya da Jamus.

Duk da matsayin Najeriya na zama kasa ta 3 da aka fi cin naman karen, a watan Yulin bara akalla mutane 18,000 suka sanya hannu akan wata takardar korafi inda suka bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatin sa da su haramta cin naman karen da kuma sayar da shi.

RFI ya ruwaito cewa naman karen dai yana da matsayi sosai a wasu jihohin Kudancin Najeriya da suka hada da Akwa Ibom da Cross Rivers da kuma Rivers inda ake masa lakabi da 404.