✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ce ta 4 a jerin kasashen da suka fi cin bashi —Bankin Duniya

Najeriya ta kasa rage ko dan wani kaso na bashin da ake binta.

Bankin Duniya ya sanar cewa Najeriya ce ta hudu a jerin kasashen duniya da suka fi cin bashi.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin rahotonsa na bana da bankin ya fitar, yana mai cewa ya zuwa ranar 30 ga Yunin 2022, yana bin Najeriya bashin Dala biliyan 13.

Bayanan sun ce ya zuwa Yunin 2021, Najeriya ce ta biyar a jerin kasashen duniya da suka fi cin bashi, wanda nauyinsa ya kai Dala biliyan 11.

Alkaluman sun nuna cikin shekara guda, Najeriya ta ci bashin da ya kai Dala biliyan 13 ($1.3bn) daga bankin wanda hakan ya sa ta maye gurbin kasar Vietnam a zama kasa ta hudu a jerin kasashen da suka fi cin bashin.

Jaridar Punch ta ruwaito Bankin na cewa, wannan bashin daban yake da bashin Dala miliyan 486 ($486m) da Najeriya ta ciyo a bankin don aiwatar da wasu manyan ayyukan gina kasa.

Kazalika, bayanan sun nuna cewa, kasashe biyar da ke kan gaba ta fuskar yawan bashin, sun dan rage nauyinsa in ban da Najeriya.