✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Najeriya ce ta daya a karfin tattalin arziki a Afirka —IMF

Najiya ta fi kowace kasa a nahiyyar Afrika bunkasar tattalin arziki.

Hukumar Bayar da Lamuni ta Duniya (IMF) ta bayyana Najeriya a matsayin kasa ta farko wajen habakar tattalin arziki a Nahiyar Afirka.

Hukumar ta bayyana haka ne bayan tantance ma’aunin hada-hadar tattalin arziki na cikin gidan kowace kasa (GDP).

A shekarar 2020 da ta kare a ranar Alhamis ta makon jiya, Hukumar IMF ta fitar da jadawalin tattalin arzikin duniya inda ta bayyana Najeriya a matsayin kasa ta 26 a duniya wajen bunkasar tattalin arzikin na cikin gida (GDP) da ta kai ta Dala miliyan 442 da 976.

Kasar da ta zo ta daya a jadawalin ita ce Amurka da GDP Dala biliyan 20 da miliyan 807 da dubu 269, sai China ta zo ta biyu da Dala biliyan 14 da miliyan 860 da dubu 775.

Kasar Japan ta zo ta uku da Dala biliyan 4 da miliyan 910 da dubu 580, sai Jamus ta hudu da Dala biliyan 3 da miliyan 780 da dubu 553, sai kuma Birtaniya ta biyar da Dala biliyan 2 da miliyan 638 da dubu 296.

Sauran su ne, Indiya mai Dala biliyan 2 da miliyan 592 da dubu 583, sai Faransa Dala biliyan 2 da miliyan 551 da dubu 451, sai Italiya Dala biliyan 1 da miliyan 848 da dubu 222 sai Canada Dala biliyan 1 da miliyan 600 da dubu 264.

A jadawalin Najeriya ce kasa ta 26 a duniya bayan ta rufa wa Beljiyum baya wadda ke da Dala miliyan 503 da dubu 416.

Hukumar tana fitar da kiyasin hada-hadar da kasashen suka yi a cikin gida wadanda cibiyoyin kudi da kididdiga suke gudanarwa, ta hanyar lissafin kasuwancin da aka yi da kuma canjin kudade da ake gudanarwa.

Sai dai wannan lissafin bai hada da yadda mutanen kowace kasa ke gudanar da rayuwarsu ba, sannan wannan jadawali yana iya canjawa duk shekara, ya danganta da hada- hadar kudi da aka gudanar a kowace kasa.

Wannan sauyin hada-hada, babu alfanu da yake da shi kan yadda al’ummar kowace kasa ke gudanar da rayuwarta ta yau da kullum.

Gwamnatin Tarayya ta dauki matakan habaka tattalin arziki ta hanyar tallafa wa sassan da suke da alaka da rayuwar ’yan Najeriya kai-tsaye. Shirin tayar da komadar tattalin arziki da gwamnati ta fito da shi (ERGP) ya mai da hankali ne wajen magance matsalar da tattalin arziki ke fuskanta ta hanyar karfafa masana’antu masu zaman kansu.

Haka zalika shirin zai bunkasa bangaren walwalar jama’a, sannan zai sanya kasuwanni su numfasa kamar yadda Tsarin Mulkin 1999 ya yi tanadi, wajen samar da sauki da walwala ga ’yan Najeriya.

Muhimman abubuwan da shirin ERGP ya fi mai da hankali a kai shi ne; karfafa bangarori masu zaman kansu da kuma samar da walwalar jama’a da hadin kan kasa da barin kasuwa ta rika numfasawa.