✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Najeriya ce ta fi yawan yara marasa zuwa makaranta’

Yara miliyan 10 na gararamba ba sa zuwa makarantu.

Minista a Ma’aikatar Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, ya ce Najeriya ta dama sauran kasashen yankin Saharar Afirka ta shanye, wajen yawan kananan yara marasa zuwa makaranta.

Nwajiuba ya ce kananan yara akalla miliyan 10 ne ke garambata a tituna ba sa zuwa makaranta a Najeriya, saboda matsalolin da suka yi wa bangaren ilimin kasar katutu.

Ya ce bugu da kari, “Muna da karancin kwararrun malamai, da karancin kayan koyarwa da kuma rashin wadatattun kudade.”

A cewarsa, matsalolin sun sa ana yanke tsammani a bangaren, duba da yadda ake fama da matsalar jahilci da gurbacewar tsari, da sauran matsaloli.

Ministan ya bayyana hakan ne a taron kaddamar da shirin “Inganta Aikin Samar da Ilimi ga Kowa (BESDA)”, a Katsina a ranar Litinin.

Ya ce shirin Ilimi na BESDA da Gwamnatin Tarayya ta kaddamar zai karade jihohi 17 a fadin Najeriya.

Daukacin jihohi 13 na yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas ne za su amfana da shirin, sai kuma jihohin Neja da Oyo da Ebonyi da kuma Ribas.

Nwajiuba ya yaba wa Gwamnan Katsina, Aminu Masari, game da kokarinsa na inganta bangaren ilimin jihar, domin cin moriyar arzikin mutane da Allah Ya huwace wa jihar.

A nashi bangaren, Masari ya yaba da hangen nesan Gwamnatin Tarayya na bullo da shirin na BESDA domin bunkasa harkar ilimi a Najeiya.