✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya da China sun kulla yarjejeniya kan yaki da ‘yan ta’adda

Najeriya ta kulla yarjejeniyar fahimtar juna da Kasar China kan yaki da 'yan ta'adda.

Gwamnatin Najeriya ta kulla wata yarjejeniyar fahimtar juna da Hukumar Dake Kula da Sojojin Kasar China kan yaki da ‘yan ta’adda.

Hakan ya biyo bayan sanya hannu kan kulla wata alaka da kasashen biyu suka yi a Shelkwatar Tsaro ta Kasa dake Abuja, sakamakon bukatar da Najeriya ta yi na neman taimakon agajin Sojoji daga kasar ta China.

Ministan Tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi (mai ritaya),da Mukaddashin Jakadan Kasar China a Najeriya, Mr Zhao Yong ne suka rattaba hannun a madadin kasashen biyu.

Magashi ya ce babu tantama idan Najeriya ta sami taimakon sojoji daga kasar China zai taimaka mata wurin kawo karshen ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ministan ya bayyana cewa, ya ji dadi da aka fahimci cewa matsalar tsaro da ta’addanci matsala ce da ta addabi duniya ba iya Najeriya kadai ba.

A don haka ya ce akwai bukatar a hada kan dukkan kasashe wuri guda don yakar ayyukan ta’addanci.

Ministan tsaron ya bukaci sauran kasashen dake makotaka da Najeriya da su yi koyi da China wurin bai wa Najeriya taimakon jami’anta na soji, saboda ta hanyar hada hannu ne kadai za a cimma yakar ‘yan ta’addar cikin kankanin lokaci.

Yayin zaman kulla yarjejeniyar, kasar China ta samu wakilcin Mukaddashin ofishin Jakadancin China a Najeriya, Mr Zhao Yong da kuma Senior Colonel Liu Yongxuan