✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya da Ghana: Gwamnati ta ba da umarnin rufe ofisoshi da wuri

Hukumar CAF ta amince a cika filin wasan makil da 'yan kallo.

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe ofisoshin gwamnati a Abuja tun daga karfe 1 na ranar Talata saboda wasan kwallon kafa da za a fafata tsakanin Najeriya da Ghana.

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne domin nuna goyon baya ga wasan neman gurbin shiga gasar Cin Kofin Duniya da tawagar Super Eagles za ta kara da Black Stars ta Ghana.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ya fitar da ke cewa tawagar ta Najeriya na bukatar magoya baya yayin fafata wasan mai mutukar muhimmaci da zai kare martabar kasar.

Najeriya da Ghana za su fafata a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja a yammacin wannan Talata, a wasan da ake sa ran ya yi zafi tsakanin kasashen biyu da ke hamayya na shekaru 71 da fafatawa 58.

Wannan wasan dai zai gudana ne bayan haduwar da ka ayi tsakanin bangarorin biyu ranar Juma’a a Kumasin Ghana da aka karkare mintuna 90 babu wanda ya ci wani.

Tuni dai Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka CAF ta lamunce a cika filin wasa na Moshood Abiola da yan kallo wanda ke daukar mutum dubu sittin.