✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya da Nijar za su hada hannu su yaki ta’addanci — Bazoum

Shugaban ya ce, mutanen Najeriya da na Nijar na da al'adu masu kamanceceniya da juna.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da takwaransa na Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum sun ce kasashen biyu sun amince su yi aiki tare don yaki da taladdanci.

Shugabannin sun bayar da wannan tabbacin ne ranar Litinin yayin da Buhari ya karbi bakuncin a wata ziyararsa irinta ta farko zuwa Najeriya tun bayan da ya dare karagar shugabancin kasar.

“Zamu bunkasa yankinmu, don amfanuwar kasashen biyu,” inji Shugaba Buhari, ta bakin Kakakinsa, Femi Adesina.

Shugaban Kasar ya ce, mutanen Najeriya da na Nijar na da al’adu masu kamanceceniya da harshe da tsarin gudanar da rayuwa.

“Muna musayar iyakar kasa mai fadin akalla kilomita 1,500 na hanyoyin kan tudu, don haka ba zamu iya watsi da juna ba,” inji Buhari.

Buhari, ya kuma taya Shugaba Bazoum murnar nasarar da ya samu a zaben Shugaban Kasar ya yi, yana mai ba da tabbatacin Najeriya na taimakawa makociyar kasar tata a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

A nasa jawabin, Shugaba Bazoum, ya yi karin haske kan dalilin da yasa ya zabi Najeriya a matsayin kasar da ya fara kawo ziyara, inda yace kasashen biyu suna da bukatu kusan iri daya don haka samun kyakkyawar alaka nada matukar muhimmanci.

“Don haka akwai bukatar samun hadin kai don tunkarar kalubalen tsaro da muke fuskanta baki daya,” inji Bazoum.