✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ga kamfanin Google: Ku hana IPOB amfani da dandalinku

Gwamnatin Tarayya ta roki kamfanin sadarwa na Google ya dakatar da ba mambobin haramtacciyar kungiyar nan ta IPOB damar amfani da dandalinsa. Ministan Yada Labarai…

Gwamnatin Tarayya ta roki kamfanin sadarwa na Google ya dakatar da ba mambobin haramtacciyar kungiyar nan ta IPOB damar amfani da dandalinsa.

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Kai Mohammed ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis, ga tawagar kamfanin da ta kai masa ziyara.

Ya ce kungiyar ta IPOB da ke rajin kafa haramtacciyar kasar Biyafara, na amfani da dandalin domin yada ta’addanci da wargaza zaman lafiya a Najeriya.

“Muna rokon Google da ya duba yadda za a haramta amfani da boyayyen shafi a dandalin YouTube ga kungiyoyin ’yan Ta’adda, da ma duk wata kafa ko wasikar yanar gizo da ke dauke da sunan haramtacciyar kungiyar da mukarrabanta,” inji shi.

Ministan ya ce a kwanakin baya ne gwamnati ta gabatar da wata dokar ka’idojin amfani da kwamfuta da intanet, don takaita makamantan wadannan matsalolin na intanet a Najeriya.

A nasa bangaren, Daraktan Google mai kula da al’amuran gwamnati da manufofin jama’a a kasahen Afirka, Charles Murito, ya ce dandalin ya bullo da wani shiri mai suna “Trusted Flaggers” ga ’yan kasar da ke da horan bibiyar abubuwan da ke intanet, don zakulo irin wadannan matsalolin.

Shi ma Manajan kula da harkokin gwamnati da tsare-tsare na Google, Adewolu Adene, ya ce karkashin sabon tsarin Google News Initiative Challenge, kafofin watsa labarai 30 na duniya, ciki har da biyar daga Najeriya, da dandalin binciken kwakwaf na Dubawa, za su samu talafin Dala miliyan 3.2, bisa kokarinsu na kirkirar sabbin hanyoyin watsa bayanai.

Ya kuma ce kamfanin zai yi aiki tare da Ma’aikatar Yada Labarai da Al’adu wajen cefanar da wasu kayan tarihi da aka dawo da su Najeriya, ta hanyar amfani da fasahar habaka kirkira da fasaha ta Google.