✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Najeriya ke da kashi 75 na laifuka a Tekun Guinea

Shugaba Buhari zai kaddamar da sabon tsarin tsaron teku a watan Yuni.

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce Najeriya ce ke da kashi kusan kashi 75% na manyan laifukan da ake aikatawa a kan ruwan Tekun Guinea.

Amaechi, yayin karbar bakuncin jakadan kasar Belgium a Najeriya, ya ce Shugaba Buhari zai kaddamar da sabon tsarin tsaron teku a cikin watan Yunin 2021.

Ministan ya ce: “Matsalar da ke addabar yankin Tekun Guinea shi ne rashin tsaro wanda ya fi yadda duniya ta sani rikitarwa.”

“Kashi 75% ko 65% na manayan laifukan na zuwa ne daga yankin tekunmu kuma idan za mu iya kawar da laifukan, to za mu samu ci gaba sosai.”

Ameachi ya bayyana cewa amma Gwamnatin Tarayya ta samar da mafita wanda a shirye take ta fara aiki.

“Sabon tsarin ya kunshi Rundunar Sojin Ruwa, ’Yan Sanda, Sojin Kasa da kuma Hukumar Tsaron Farin Kaya ta SSS.

“Idan tsarin ya yi nasara, a nan gaba, za a samu ci gaba a harkar tsaron teku, daga nan kuma wasu kasashen yankin Tekun Guinea za su iya rungumarsa,” inji Amaechi.

“Daga jirgin sama, za ka ga abin da ke faruwa a cikin teku, idan ma kana cikin ruwa za ka iya ba da dauki. Duk sadda aka ga abin da ya a yarda da take-takensa ba a kan teku, helikofta zai iya zuwa ya saukar da sojojin ruwa a wurin,” inji shi.