✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya na dab da samo maganin COVID-19 —Minista

Ministan Kimiyya da Fasaha Dokta Ogbonnaya Onu ya kaddamar da wani kwamiti a kan magungunan gargajiya da kokarin na samo maganin cutar COVID-19 a gida…

Ministan Kimiyya da Fasaha Dokta Ogbonnaya Onu ya kaddamar da wani kwamiti a kan magungunan gargajiya da kokarin na samo maganin cutar COVID-19 a gida Najeriya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa kwamitin ya kunshi fitattun masana ilimin kimiyya karkashin kungiyar NAS .

Ministan ya ce an kafa kwamitin ne domin tantance ikirarin da wasu masu bincike, masana kimiyya da masu magungunan gargajiya wajen maganin cutar.

Ya ce ma’aikatarsa ta dukufa wajen kirkirowa da inganta magungunan da za a yi amfani da su a matsayin rigakafin cutar.

Dokta Ogbonnaya ya ce, “Muna son mu kara jaddada alkawarinmu na bayar da Naira miliyan 30 ga duk dan Najeriyan da ya yi hobbasa wajen gano maganin da zai kai ga zama kariya daga cutar.”

Ministan ya bukaci kwamitin da ya jajirce wajen tantance duk abun da aka kawo masa da nufin ganin aikinsa ya haifar da da mai ido.

Ya ce yunkurin ya yi daidai da kudurin Shugaba Buhari na ganin an fadada hanyoyin samar da kudaden shiga.

Ya kuma ce har yanzu cutar babbar barazana ce ga rayuwa da tattalin arzikin ‘yan Najeriya.

Shugaban Kwamitin, Farfesa Mosto Onuoha ya yi alkawarin cewa kwamitin zai ba mara da kunya wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata.