✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Najeriya na fuskantar barazanar tsaro mafi girma tun bayan Yakin Basasa’

Ya ce duk da yake akwai kalubale, amma Buhari ya yi nasara

Gwamnatin Tarayya ta ce tabarbarewar tsaron da ake fama da ita a halin yanzu ita ce kalubale mafi girma ga zaman lafiya da tsaro a Najeriya tun bayan kammala Yakin Basasa.

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a yayin wani taron hadin gwiwa na harkar tsaro da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin.

Ya ce, “kalubalen tsaro ya kasance mai ban tsoro, tun daga ta’addanci zuwa yin garkuwa da mutane zuwa tashin hankalin ’yan aware zuwa satar danyen mai zuwa fashi da makami da kuma laifuka iri-iri.

“Babu shakka shi ne babban kalubale ga zaman lafiya da tsaron kasarmu mai girma tun bayan kammala Yakin Basasa da aka yi daga shekarar 1967 zuwa 1970.”

A cewar Ministan, irin wannan kalubale ne da zai mamaye kasashe da dama, “amma godiya ga kyakkyawar jagoranci na Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, muna iya cewa sannu a hankali zaman lafiya da tsaro suna dawowa a kasar.

“Don Allah kar ku yi kuskure ko ku yi wa wannan ikirari mummunar fahimta. Har yanzu muna iya shaida kebance lokuta na kalubalen tsaro a nan da can, amma ba zai kasance a kan sikelin da muka gani a baya ba.

“Muna so mu yi amfani da wannan damar mu jinjina wa Shugaban Kasa bisa jagorancinsa.

“A lokacin da wasu da dama suka yi kira da a yi amfani da sojojin haya na kasashen waje wajen tunkarar kalubalen da ake fuskanta, musamman ta’addanci da ’yan fashi da makami, Shugaba Buhari bai taba yin kasa a gwiwa ba wajen aminta da yadda dakarunmu maza da mata suke sanye da kakinsu suka tashi tsaye wajen ganin sun yi nasara .

“Wasu sun ce kalubalen tsaro ya mamaye sojoji, amma a yanzu sojoji sun nuna cewa babu wata kungiyar ’yan ta’adda da za ta iya mamaye su.