✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya na iya wargajewa idan ba a addu’a

Akwai mutane masu mugun nufi da ba su son a zauna lafiya a Najeriya

Tsohon Shugaban Kasan Najeriya Yakubu Gowon ya yi zargin cewa akwai miyagu marasa son ganin an samu zaman lafiya a kasar.

Gowon ya bukaci ‘yan Najeriya su dage da yi wa kasar addu’o’i domin kare ta daga wargajewa.

Tsohon shugaban ya haka ce ta sa duk da kokarin da Shugaba Buhari ke yi, har yanzu matsalar tsaro a kasar ta ki karewa.

“Muna bukatar zaman lafiya domin ci gaba. Na san Shugaba Buhari na yin iya kokarinsa amma har yanzu galibin matsalolin ba su kau ba.

“Akwai mutane masu mugun nufi da ba su son zaman lafiya.

“Ina rokon CAN da ta ci gaba yin addu’o’i ba wai ga Yakubu Pam kadai ba, har da Shugaban Kasa da ma dukkaninmu da kasarmu, domin kada Najeriya ta wargaje”, inji tsohon shugaban.

Ya yi bayanin ne a taron nuna godiya da Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta shirya wa sabon Babban Sakataren Hukumar Ziyarar Kirista ta Najeriya Rev. Yakubu Pam, a Abuja.

Gowon ta bakin Ministan Ayyuka na Musamman da Huldar Hukumomi, George Akume, wanda ya wakilce shi a taron ya ce “matsalolin Najeriya za su zarce na kasar Somalia, muddin aka yi nasarar yi wa ‘yancin kasar zagon kasa.