✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya na iya wargajewa idan ba a sauya tsarinta ba —Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi gargadin cewa Najeriya za ta ci gaba da zama cikin halin rashin tsaro rashin ci gaba da tabarbarewar…

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi gargadin cewa Najeriya za ta ci gaba da zama cikin halin rashin tsaro rashin ci gaba da tabarbarewar al’amura muddin aka ki sauya fasalin yadda ake tafiyar da kasar yanzu haka.

Obasanjo ya ce duba da yadda nauyi ya yi wa Gwamnatin Tarayya yawa musamman ta bangaren tsaro, sauya tsarin shugabancin kasar ya zama wajibi.

Ya fadi hakan ne yayin wata lacca da aka saba gudanarwa duk shekara ta Sobo Sowemimo da ta gudana ta fasahar bidiyo a birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Taken laccar ta bana dai da wata kungiya mai suna Abeokuta Club ta shirya shi ne, “COVID-19: Ina mafita ga kalubalen tsaron Najeriya?”.

Obasanjo wanda ya zargi gwamnatoci a dukkanin matakan Najeriya da gazawa ya ce yanzu ba lokacin da za a zauna a ci gaba da kallon abubuwa na kara tabarbarewa ba ne.

A cewarsa, “Ci gaba da nuna wa juna yatsa ba zai kawo maslaha ba, kazalika raba kasa ita ma ba mafita ba ce, kamar yadda ci gaba da yin shiru shi ma ba zai haifar wa kasar da mai ido ba.

“Makomar kasar nan tana hannun maza da mata masu kwarin gwiwa, kishin kasa da kuma hangen nesa su zo su ja ragamarta.

“Kin yin wani abu yanzu ba zai haifar wa Najeriya da mai ido ba, idan abubuwa suka ci gaba da tabarbarewa hakan zai iya tunzura mutane su nemi ballewa. Allah ya kiyaye wannan ranar”, inji Obasanjo.

Abin da ya kamata bayan COVID-19

Da yake bayani a kan yanayin kasar bayan wucewar annobar coronavirus, tsohon shugaban kasar ya ce kamata ya yi a mayar da hankali wajen samar da abinci, tsaro, da kuma bunkasa tattalin arziki.

“Ina da yakinin tattalin Afirka za ta bunkasa bayan gushewar wannan annobar.

“Amma kamar mu a Najeriya ba mu da wani zabi da ya wuce mu yi abin da ya dace.

“Idan kuwa ba mu yi abun da ya dace ba yanzu, to tabbas yanayin da za mu tsinci kanmu nan gaba ta bangaren tattalin arziki da tsaro sai ya fi wanda muke ciki yanzu muni.