✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gwamnati ke leken asirin wayoyin ’yan Najeriya

Akalla hukumomi biyu na amfani da na’urorin leken asiri daga Isra'ila

Wani rahoto ya bankado yadda hukumar tara bayanan tsaron lafiyar kasa ta Najeriya (DIA) ke amfani da kayan leken asiri a fadin kasar.

Hakan na kunshe ne a rahoton da cibiyar bincike kan leken asiri, tsaro da adalci ta fasahar zamani ta Citizen Lab a Jami’ar Toronto ta kasar Canada ce ta fitar.

Rahoton ya ce akalla hukumomin Gwamnatin Najeriya biyu ne ke amfani da na’urorin kamfanin na Circles mai alaka da kasar Isra’ila.

“Mun gano wurare biyu da ke amfani da kayan Cirles a Najeriya; na farkon an ajiye shi ne a daidai inda muka gano manhajar leken asiri ta kamfanin FinFisher a watan Dismban 2014”, inji Citizens Lab.

Ya ce ci gaba da cewa da alama na biyun mallakin Hukumar Tara Bayanan Sirri ta Hedikwatar Tsaro (DIA) ne saboda “adireshinsa ya nuna Hedikwatar DIA da ke Asokoro, Nigeria, Abuja”.

Citizen Lab ya ce kasashe 25, ciki har da Najeriya sun sayi kayan leken asirin wayoyin ’yan adawa, masu bore, ’yan jarida da tsageru a kasashensu daga kamfanin Circles.

Circles reshe ne na kamfanin kasar Isra’ila mai suna NSO Group mai yin manhajar leken asiri ta Pegasus wadda gwamnatoci ke amfani da ita suna daukar bayanan masu bore ta hanyar kutse a wayoyinsu da sarrafa kyamara da makirfon wayoyin.

Circles ta kuma sayar wa kasashe da fasahar SS7 mai ba da damar hada layukan sadarwa daban-daban.

Ana kuma iya hada manhajojin Circles da na NSO Group su yi aiki a matsayin guda daya.

Rahoton ya bayyana cewa: “Sabanin manhajar Pegasus ta leken asiri na NSO Group, ita SS7 ta Circles ba ta nuna wata alama a kan wayar da aka yi wa kutse”.

Zuwa yanzu dai gwamnatin Najeriya ba ta ce uffan kan rahoton na Citizen Lab wanda ya ce masu gwagwarmaya na fuskantar barazana ta fasahar sadarwar zamani ta fuskoki da dama.

Wani rahto na Kwamitin Kare ‘Yan Jarida (CPJ) ya nuna yadda gwamnatin kasar ke wuce gona da iri wurin bibiyar wayoyi a kasar.