✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya na neman diyyar ‘gurbataccen abincin’ da aka ba alhazanta a Saudiyya

Najeriya ta ce an sami matsalar ce saboda ba ita ta bayar da abincin ba

Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta ce za ta nemi hukumomin kasar Saudiyya su dawo mata da kudin abincin alhazanta saboda ta ba su gurbataccen abincin.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Laraba, ta ce Shugabanta na kasa, Zikrullah Kunle Hassan ne ya bayyana haka a Muna, da ke Saudiyya, lokacin da ziyarci tantunan alhazai na jihohi.

Ya ce tuni suka rubuta wasika zuwa ga hukumomin Saudiyya da suka kamata kan yanayin abincin da aka ba alhazan wanda suka yi ta korafi a kan ingancinsa.

Rashin abinci mai kyau dai na daya daga cikin tarin matsalolin da suka yi wa alhazan Najeriya katutu yayin aiki Hajjin na bana.

A cewar Zikrullah, an sami matsalar abincin a Muna ne saboda hukumomin Saudiyya ne suka karbe ragamar ciyar da alhazan, sabanin yadda ake yi a baya.

Shugaban ya kuma yaba wa alhazan kan hakuri da fahimtar da suka nuna duk da tarin kalubalen, yana mai cewa Aikin Hajji dama ya gaji jarabawa iri-iri.

Daga nan sai ya hore su da su ci gaba da kasancewa jakadun Najeriya na gari, a ragowar lokacin da ya rage musu a can.