✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta fi kowacce kasa yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya – UNICEF

“A cikin kowanne yara biyar da ba sa zuwa makaranta a duniya, daya daga cikinsu dan Najeriya ne.”

Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce akwai yara kimanin miliyan 10.5 da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, alkaluman da suka fi na kowacce kasa yawa a fadin duniya.

Jami’in hukumar a Najeriya, Peter Hawkins, ne ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar domin bikin Ranar Ilimi ta Duniya ta bana.

Sai dai ya jinjina wa Gwamnatin Najeriya kan alkawarin da ta yi na kara kasafin kudinta a kan harkar ilimi da kaso 50 cikin 100 a shekaru biyu masu zuwa, da kuma kaso 100 nan da 2025.

Ya lura cewa akwai miliyoyin kananan yara a Najeriya da ko taka aji ba su taba yi ba, kari a kan mummunar illar da annobar COVID-19 ta yi wa harkar ilimi a kasar.

Sanarwar ta ce, “A kasafin kudin Najeriya na 2022 wanda ya kai Naira tiriliyan 17, kaso 7.2 aka ware wa bangaren ilimi. Wannan mataki ne mai kyau, duk da dai akwai sauran tafiya kafin a kai ga cimma muradun kasa da kasa na kaso 15 zuwa 20 a kasafin kowacce shekara.

“Gwamnatin Najeriya ta himmatu matuka wajen kara kudaden da take kashewa a bangaren, wannan abin a yaba ne, saboda zai kawo ci gaba matuka.

“Akwai yara miliyan 10.5 da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, wannan shi ne adadi mafi yawa a duniya.

“Alkaluman na nuni da cewa akalla kashi daya cikin uku na yaran da suke kasar ba sa zuwa makaranta, kuma a duk mutum biyar da ba sa zuwa makaranta a duniya, daya daga cikinsu dan Najeriya ne,” inji UNICEF.

Asusun ya kuma ce duk da cewa kalubalen na shafar kusan kowanne sashe na yaran a kasar wani sashe na yara sun fi fuskantar barazana.

Wadanda suka fi fuskantar kalubale a cewar UNICEF sun hada da mata da masu bukata ta musamman da ’ya’yan masu karamin karfi da kuma na ’yan gudun hijira.