✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Najeriya ta fi kowace kasa yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya – UNICEF

UNICEF ta koka kan yadda ake ci gaba da samun yaran ba sa zuwa makaranta.

Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya koka kan yadda Najeriya ke kan gaba wajen yaran da ba sa zuwa makaranta a fadin duniya.

Manajar Ilimi na hukumar da ke jihar Sakkwato, Miriam Mareso ce, ta bayyana hakan a Jihar birnin na Sakkwato.

Ta ce Najeriya na samar da daya daga cikin yara biyar da ba sa zuwa makaranta a duniya wanda kididdiga ta nuna nuna cewa gwamnati ba ta ware wasu kudade na ku-zo-ku-gani wajen kula da Ilimi da lafiya.

Miriam Mareso ta bayyana haka ne a yayin bude taron tattaunawa na kwanaki biyar kan harkokin yada labarai kan ilimin yara mata da aka shirya wa wakilan kafafen yada labarai da ke ba da rahoto a jihohin Sakkwato da Zamfara.

Mareso, ta bukaci gwamnatoci a dukkan matakai da su samar da al’umma mai wayewa, ta hanyar aiwatar da tsare-tsare na ilimin yara mata da kuma tabbatar da aiwatar da kasafin kudin da aka ware saboda hakan.

“Ana sa ran gwamnatoci a dukkan matakai su kara himma wajen aiwatar da tsare-tsare kan ilimin yara mata da kuma gano abin da ke haddasa karancin zuwansu makarantu, musamman a Arewacin Najeriya”

Manajar Ilimin ta UNICEF ta ce matsakaiciyar yarinya a Najeriya na iya samun kaso 50 cikin 100 na damar shiga makarantun Firamare da Sakandare, saboda kaso 20 cikin 100 ne kawai ake samu a makarantun firamare yayin da kuma kaso 30 cikin 100 ke shiga makarantar sakandare.

Sai dai wasu na ganin karuwar wadanda ba sa zuwa makaranta musamman yara mata, na da alaka da matsalar tsaro da ake fuskanta a yankin Arewa maso Yammacin kasar.