✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta gano gunkin tarihinta da aka sace a Mexico

Gunkin tarihin ya samo asali ne daga garin Ife na Jihar Osun.

A ranar Alhamis, Gwamnatin Tarayya ta gano wani gunkin tarihi da aka sace daga Najeriya a birnin Mexico na kasar Mexico.

An damka gunkin tarihin a hannun Ministan Harkokin Kasashen Waje, Geoffrey Onyeama.

Gunkin tarihin, ya samo asali ne daga garin Ife da ke Jihar Osun, a yankin  Kudu-maso-Yammacin Najeriya.

Onyeama, ya ce an dawo da gunkin da aka sace aka sayar da sassansa ga kasashen duniya,  gida Najeriya bayan  ya shafe tsawon lokaci ana neman sa.

Ya kara da cewa tun a 2017, tsohon Jakadan Najeriya a kasar Mexico, Aminu Alhaji Iyawa, ya fara farautar gunkin a filin jirgin sama na Benito Juarez na kasar.

A cewarsa, bayan tsaurara bincike da Ma’aikatar Yada Labarai da Raya Al’adu ta Najeriya ta yi, an tabbatar da cewa gunkin na Najeriya ne tare da dawo da shi gida, don ci gaba da raya tarihi.