✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnati ta hana jirgin Emirates shigowa Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta sanya jirgin Emirate cikin jerin wadanda ta haramtawa shigowa kasarta daga ranar Litinin, 21 ga watan Satumba, 2020. Ministan sufurin jiragen sama,…

Gwamnatin Najeriya ta sanya jirgin Emirate cikin jerin wadanda ta haramtawa shigowa kasarta daga ranar Litinin, 21 ga watan Satumba, 2020.

Ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, ya wallafa hakan a shafinsa na Tiwita @hadisirika.

Aminiya ta ruwaito cewa gabanin bude zirga-zirgar jiragen kasashen waje ranar 5 ga watan Satumba, cewar gwamnatin tarayya hana jiragen kasa 10 shigowa kasarta.

Daga cikin jiragen akwai Lufthansa, da Air France da Etihad da KLM da Air Namibia, da dai sauransu.

Haka nan kuma a daidai wannan lokacin suka bar wasu jiragen da suka hada da Emirates da Egypt Air da British Airways da Ethiopia da AWA, da sauransu su ci gaba da shigowa.

Sai dai kuma a daren jiya Ministan ya bayyana cewar an haramtawa jirgin Emirates shigowa, wanda hakan ya sa ya fita daga jerin jiragen da aka aminta su shigo can baya.

Sirika ya ce matakin ya biyo bayan taron da suka yi ne da karamin kwamitin shugaban kasa na yaki da annobar COVID-19 da Jakadan Kungiyar Tarayyar Turai (EU).

Wakilin ya jiyo cewar Ambasada Ketil Karlsen, wanda shi ne babban jami’in EU a Najeriya da ECOWAS, ya jagoranci jakadun kasashen turan zuwa taron da aka gudanar.

Makasudin taron shi ne, gwamnatin tarayya ta kara yin duba da matakin da ta dauka na hana shigowar jiragen daga kasashen Turai.

Sirika ya bayyana cewar an samu ci gaba a taron, sai dai an kara Emirates cikin sahun jiragen da aka hana shigowa Najeriya.

“Kwamitin da Shugaban kasa ya nada ya yi taro da jakadun kasashe ’yan kungiyar tarayyar Turai (EU), domin tattaunawa kan hana shigowar jiragen irin su Lufthansa da Air France/KLM.”

“Emirates kuma an saka su cikin jerin wadanda aka haramtawa shigowa, daga ranar Litinin, 21 ga watan satumba, 2020.”

Ana kyautata zaton gwamnatin tarayya ta dauki matakin ne sakamakon hana bayar da biza ta shiga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da gwamnatin su ta yi.

Najeriya ta sha alwashin hana jiragen kasashen da ba su yarda a shiga kasashensu ba shigowa kasarta.