✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta karbi tallafin kayan yakar coronavirus na Dala miliyan 22

Tarayyar Turai da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya sun ba wa gwamnatin Najeriya tallafin kayan yaki da cutar coronavirus da suka kai na Dalar Amurka…

Tarayyar Turai da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya sun ba wa gwamnatin Najeriya tallafin kayan yaki da cutar coronavirus da suka kai na Dalar Amurka miliyan 22.

Kayan sun hada da na gwajin cutar guda 100,000, na’urorin adana iskar numfashi guda 545, na’urorin gwada zafin jiki, rigunan kariya da kuma sauran kayan amfani a dakunan gwaje-gwajen cutar.

Bayanin hakan na kunshe ne a wata sanarwa da jami’in yada labarai na tawagar Tarayyar Turai a Najeriya, Modestus Chukwulaka ya fitar a ranar Asabar a Abuja.

A cewar sanarwar, tallafin zai taka rawa sosai wajen kokarin gwamnati na yaki da cutar musamman ga wadanda suka riga su ka kamu da ita.

Sanarwar ta ce kimar kayan tallafin da ma wadanda za su biyo bayansu nan ba gaba ta haura Dalar Amurka miliyan 22.

“Wadannan kayan tallafin za su taimaka wa gwamnatin Najeriya wajen yaki da cutar, kara yawan wadanda ake iya gwadawa a kullum da kuma gano ta tun da wuri.

“Tallafin da muka damka wa Najeriya ta hannun Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) da kuma Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA) mun kuma gabatar da shi a hukumance ga Kwamitin Kar-ta-kwana Da ke yaki da cutar a wani taro da wakilan Majalisar Dinkin Duniya, Tarayyar Turai da kuma Ma’aikatar Lafiya ta Najeriya suka halarta”, in ji sanarwar.

Jami’in kula da jinkai na MDD a Najeriya, Mista Edward Kallon ya ce kayan za su taimaka wa Najeriya matuka a yakin da take yi da cutar.

Ya ce zuwa yanzu, Tarayyar Turai ta bi sahun sauran hukumomi da kasashen duniya wajen tallafa wa kasar da Euro miliyan 50 ta hannun asusun tallafin yaki da cutar a Najeriya a matsayin ta su gudunmawar don yakar annobar.