✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kashe Triliyan N3.2 Da Muka Kwato Daga Barayin Gwamnati —Malami

Gwamnatin Tarayya ta samu ta samun Naira biliyan 1.82 daga kadarorin sata da ta kwato

Najeriya ta kwato Naira triliyan 3.2 na tsabar kudin da aka sace daga kasar daga shari’oi daban-daban a duniya.

Wannan bayani ya fito ne daga Babban Lauyan gwamnati kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, a ganawarsa da ’yan jarida a Fadar Shugaban Kasa a ranar Alhamis.

Wadannan kudadde, a cewarsa, Ma’aikatarsa ce ta jagoranci kwato su daga shari’o’i da ta wakilci Gwamnatin Tarayya a kasashen duniya a tsakanin watan Maris na 2021 da watan Mayu na 2022.

Ministan ya ce tuni aka zuba kudaden a ayyukan raya kasa a wurare daban-daban a fadin kasar nan, ciki har da ginin gada 2nd Niger, da aikin hanyar Abuja zuwa Kano, da kuma ta Legas zuwa Ibadan.

Ya ci gaba da cewa, Gwamnatin Tarayya ta samu Naira biliyan 1.82 daga sayar da takardun lamuni da kuma sayar da wasu kadarorin gwamnatin da aka kwato a watanni 18 da suka gabata.

Malami ya kara da cewa, Ma’aikatar  Shari’a ta mara wa gwamnati baya wajen kulla yarjejeniyar samar da kudaden gudanar da wasu ayyukan ci gaba.

Wannan hira da ‘yan jaridu da Ministan ya halarta, shi ne kashi na 46 a cikin jerin hirarrakin da Kwamitin Yada Labarai na Fadar Shugaban kasa ke shiryawa a Abuja.