✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Najeriya ta sami tiriliyan 1.3 ta hanyar noman rake a shekara 10

Kudaden sun hada da na nomanta da kuma na sarrafa ta

Najeriya ta sami kudaden da suka haura Naira tiriliyan daya da biliyan 300 ta hanyar noman rake a shekara 10 da suka gabata.

Shugaban Hukumar Bunkasa Sukari ta Kasa (NSDC), Zacch Adedeji ne ya bayyana hakan yayin bikin sanya hannu a kan yarjejeniya tsakanin kamfanin Saro Africa Group da Gwamnatin Jihar Nasarawa.

Yarjejeniyar dai ta tanadi gina kamfanonin sarrafa rake a Kananan Hukumomin Doma da Nasarawa na Jihar.

A cewar Shugaban hukumar, kudaden sun hada da ainihin wadanda aka samu a noman raken da kuma wadanda aka zuba jarinsu wajen sarrafa ta.

Ya ce ta hanyar aiwatar da Shirin Bunkasa Sukari na Najeriya (NSMP) bangaren ya samu masu zuba jari har biyar da suka shiga harkar ka’in da na’in.