✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta shigo da danyen sukari na N410bn cikin shekara daya

Sai adadin ya ragu a watanni ukun karshen shekarar

Alkaluman Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) sun nuna cewa daga tsakanin watanni shidan karshe shekarar 2021 zuwa watanni shidan farkon 2022, Najeriya ta shigo da danyen sukarin da ya kai na Naira biliyan 410 da miliyan 600.

Sinadarin dai wanda shi ne jigo wajen hada sukari na cikin kayayyakin da Babban Bankin Najerya (CBN) ya ke takaita bayar da kudaden waje don shigo da su.

Kazalika, yana daya daga cikin kayayyaki 10 da aka fi shigowa Najeriya da su daga ketare, galibi daga kasar Brazil.

Alkaluman dai na nuna cewa an shigo da sinadarin na Naira biliyan 114 a watanni ukun na biyun shekarar 2021 daga Brazil da Adorra, sai kuma na Naira biliyan 135 a watanni ukun tsakiyar 2021.

Sai dai a watanni ukun karshen 2021 da watanni ukun farkon 2022, adadin sinadarin da ake shigowa da shi ya ragu zuwa biliyan 85.3 da kuma Naira biliyan 81.5.

Aminiya ta gano cewa ragin ba zai rasa nasaba da yunkurin da Najeriya ke kokarin yi wajen tabbatar da cewa kamfanonin sukari guda hudu na kasar suna samar da shi daga gida don rage dogaro da kasashen ketare.

A shekarar 2023 ne Najeriya ta kaddamar da manufar sukari ta kasa don inganta noman rake a kasar don rage shigo da ita daga ketare.

A cikin shekara 20 da suka gabata dai, Najeriya ta sami nasarar rage adadin sukarin da ake shigo da shi bayan kafa kamfanonin sukari na Dangote da BUA da kuma Golden Super.