✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta tafka asarar tiriliyan 3 sanadiyyar ambaliya a bara —Gwamnati

Sai dai ta ce duk da haka, barnar ba ta kai ta 2012 ba

Ministar Jinkai da Walwalar Jama’a, Hajiya Sadiya Umar Farouk ta ce jimlar asarar da Najeriya ta tafka a sanadiyyar ambaliyar ruwa a shekarar 2022 ta haura ta Naira tiriliyan uku.

Ta ce an tattara alkaluman ne daga farkon shekarar zuwa ranar 25 ga watan Nuwamba.

Da take jawabi a karshen mako a Abuja yayin gabatar da wani rahoto kan ambaliyar, ta ce wuraren da barnar ta shafa sun hada da gidaje da sauran gine-gine da ma gonaki.

Sai dai ta ce duk da haka, barnar ba ta kai wacce aka fuskanta a shekara ta 2012 ba.

Ministar ta kuma ce adadin mutanen ya zuwa karshen watan Yunin sun kai mutum miliyan 4.4, inda zuwa watan Nuwamba suka kai miliyan 4.9, adadin da ta ce ya kai kusan kaso biyu cikin 100 na yawan mutanen kasar.

“Ta bangaren lalacewar gine-gine kuwa, jihohi da dama sun fuskanci matsalar, kuma har yanzu muna ci gaba da tattara alkaluma. Kayyyakin wutar lantarki da na ruwa da suka haura na Dala biliyan 1.23 ma sun salwanta,” in ji ta.

Minista Sadiya ta kuma ce Jihohin da lamarin ya fi yi wa illa sun hada da Jigawa da Ribas da Taraba da Kuros Riba da Bayelsa da kuma Delta.

Ta kuma ce hekta 650,000 na amfanin gona ta lalace sanadiyyar ambaliyar, kodayake wasu alkaluman na nuna cewar akwai yiwuwar adadin ya haura zuwa hekta miliyan daya.