✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta yi kunnen doki da Cape Verde a wasan neman tikitin Gasar Kofin Duniya

A yanzu dai Najeriya ce ke kan gaba a rukunin C da maki 13 bayan wasa 6.

Kunnen doki aka yi tsakanin Najeriya da Cape Verde yayin da aka tashi wasa daya da daya a fafatawar da suka yi ta neman samun tikitin shiga Gasar Kofin Duniya.

Victor Osimhen ne ya ci wa tawagar Super Eagles kwallo a minti daya da fara wasa, sai dan wasan Cape Verde Stopira ya farke a minti 6 a karawar da ta gudana ranar Talata a filin wasa na Teslim Balogun da ke birnin Ikko.

A yanzu dai Najeriya ce ke kan gaba a rukunin C da maki 13 bayan wasa 6.

Najeriya ta ci wasa hudu ta yi kunnen doki daya, sannan aka doke ta a wasa daya.

Cape Verde ke biye mata da maki 11, wadda ta ci wasan uku, kunnen doki biyu sannan aka doke ta a daya.

Da wannan sakamakon, yanzu Najeriya za ta fafata wasan fidda gwani (play-off) domin samun shiga Gasar Kofin Duniya.