✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya tana bukatar karin ‘tsageru’ —Obasanjo

Obasanjo ya bayyana damuwa a kan yadda Najeriya ta samu kan ta a yau.

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce kasar na bukatar karin mutanen da suka amsa sunan tsagera wadanda za su rika fada wa shugabanni gaskiya ba tare da wata fargaba ba.

Obasanjo ya ce wannan shi ne mataki na farko da zai farfado da martabar kasar nan domin ciyar da ita gaba.

Aminiya ta ruwaito cewa Obasanjo na wadannan kalamai ne wajen kaddamar da wani littafi da aka wallafa a kan shugaban addinin kasar Yarbawa, Tayo Sowunmi, a birnin Abeokuta.

Tsohon shugaban, wanda ya ce babu yadda za a yi kasar ta ci gaba muddin kowa na zuba ido yana kallon abin da ke faruwa ba tare da bude baki ana magana ba, ya bayyana damuwa a kan yadda Najeriya ta samu kanta a yau.

Obasanjo ya ce ya zama wajibi ga duk wani mutum da ya tsaya wa gaskiya da amana a dinga ganin shi kamar dan tawaye saboda yadda zai dinga tsage gaskiya yana fada wa kowa.

Tsohon shugaban ya ce ba su da wata kasa da za su kira a matsayin tasu, saboda haka suna bukatar karin ‘yan tawaye wadanda za su dubi idanun shugabanni domin fada musu gaskiya ba tare da wata fargaba ba.