Najeriya tana da karancin malamai 277,537 a makarantun Firamare — UBEC | Aminiya

Najeriya tana da karancin malamai 277,537 a makarantun Firamare — UBEC

    Chidimma C. Okeke da Ishaq Isma'il Musa

Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimin Makarantun Firamare ta Kasa UBEC, Dokta Hamid Bobboyi, ya ce Najeriya tana fama da karancin malamai 277,537 a makarantun matakin ilimi na farko.

Bobboyi ya ce an gano hakan ne sakamakon wani bincike da aka gudanar tun a shekarar 2018 kan makarantun Firamare na Gwamnati da na masu zaman kansu da ke fadin kasar.

Ya ce binciken da Hukumar UBEC ta gudanar ya kara nuna yadda ake da kashi 73% na kwararrun malamai a makarantun Gwamnati da suka cancanci aikin karantarwa.

Haka kuma binciken ya nuna cewa kashi 53% ne kacal na malaman makarantun masu zaman kansu suka cancanci aikin karantaswa wadanda suka mallaki shaidar ilimin koyarwa ta NCE.

Ya ce, “fatan mu shi ne yadda gwamnati ta kawo sabbin manufofi, a samu wani tsari wanda zai kwadaitar da kwararru da suka cancanta su shiga aikin karantaswa domin kawo managarcin sauyi.”

Dokta Hamid wanda ya gabatar da jawabansa a birnin Abuja, ya ce Hukumar UBEC domin tabbatar da muhimmancin malamai wajen samar da ingataccen ilimi, ta ware kashi 10% na kudin shiga da take samu domin bunkasa ci gaban kwarewar malamai.

Ya kuma nemi dukkanin masu ruwa da tsaki da hada hannu da Gwamnatin Tarayya domin tabbatar da ingancin karantarwa da ilimi a matakin farko a fadin kasar.

Ya ce hukumar ta lura da bukatar hakan bisa la’akari da muhimmancin horas da malamai domin samun kwarewa a harkar karantaswa, lamarin da ya ce ingantacciyar hanyar karantarwa ta raja’a ne a kan kwararru da kuma nagartattun malamai da aka tanadar.

A cewarsa, babban kalubalen da ake fuskanta shi ne samun malamai wadanda suka kware kuma suka cancani karantar da yara a fadin a kasar.

Ya ce Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tana ci gaba da jajircewa wajen shawo kan wannan kalubale a yayin da a yanzu iyaye ke burin ganin ‘ya’yansu sun karanci aikin Likitanci, Shari’a, Tsimi da Tanadi, Injiniyaci da sauran fannoni na ilimi.