✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya za ta dau fansa kan rufe shagunan ’yan kasarta a Ghana

Najeriya ta yi tir da rufe shagunan ’yan kasarta kuma za ta gurfanar da Ghana a Kotun ECOWAS

Gwamnatin Tarayya ta yi Allah-wadai da rufe shagunan kasuwancin ’yan Najeriya da hukumomin kasar Ghana suka yi a ’yan kwanakin nan.

Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama ya bayyana hakan yayin tattaunawa da wata kungiyar kare martabar Najeriya karkashin jagorancin Mista Jasper Emenike.

Mista Geoffrey wanda ya kwatanta matakin da hare-haren kin jinin baki ya ce akwai yiwuwar Gwamnatin Tarayya ta yi ramuwar gayya a kan Ghana.

Ministan ya kuma ce watakila Najeriya ta kai karar Ghana a Kotun Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), muddin ta gano ta keta yarjejeniyar shige da ficen mutane a yankin ba tare da tsangwama ba.

“Za mu kira jakadanmu da ke kasar mu tattauna da shi tare da gano hakikanin abin da ya faru.

“Ba na so in yi riga malam masallaci, amma dai za mu yi dukkan abin da ya kamata bayan mun ji abin da ya faru.

“Idan har muka gano matakan sun saba da yarjeniyoyin ECOWAS, to tabbas za mu duba yiwuwar maka su a kotu.

“Muna kuma tunanin daukar matakan ramuwa, amma dai muna bi a hankali don ganin an magance matsalar cikin kankanin lokaci.

Dangantaka dai ta soma yin tsami tsakanin kasashen biyu ne tun bayan da aka rushe wani bangare na ginin Ofishin Jakadancin Najeriya a kasar a ’yan watannin baya.