✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya za ta dauki Mourinho ya zama kocin Super Eagles

NFF ta tuntubi Mourinho domin ya karbi ragamar Super Eagles.

Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta tabbatar da tattaunawa tsakaninta da tsohon kocin kungiyar Manchester United ta Birtaniya, Jose Mourinho don karbar aikin horas da kungiyar Super Eagles, bayan sallamar Gernot Rohr.

A ranar Laraba ne dai Shugaban hukumar, Amaju Pinnick, ya tabbatar da tuntubar Mourinho, wanda a yanzu shi ne kocin AS Roma da ke gasar Seria A, a kasar Italiya.

NFF na son Mourinho ya karbi Super Eagles ne a matsayin kocin dindin don kawo sabon sauyi a kungiyar.

Kazalika, NFF ta ce ta sake tattaunawa da Mladen Krstajic dan asalin kasar Sabiya da kuma Jose Peseiro dan kasar Portugal, don ganin ko za su karbi kocin Super Eagles idan Mourinho bai amince ba.

Tun bayan sallamar Rohr, NFF ta ba wa Austin Eguavoen damar rike Super Eagles na wucin-gadi zuwa bayan kammala Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka wanda za a fara a watan Janairu 2022 a kasar Kamaru.

NFF ta sallami Gernot Rohr ne a ranar 12 ga watan Disamba 2021, bayan ya shafe shekara biyar yana horas da ’yan wasan Super Eagles.