✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya za ta fara buga wa kasar Gambiya takardun kudade

Emefiele ya ce Najeriya na da karfin buga kudaden kasancewar ta fara buga nata tun shekarun 1960.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya amince ya fara buga wa kasar Gambiya takardun kudadenta na Dalasi.

Gwamnan Bankin, Godwin Emefiele ne ya amince da bukatar hakan wacce takwaransa na Babban Bankin kasar ta Gambiya, Mista Buah Saidy ya gabatar lokacin da suka ziyarce shi a ranar Talata a Abuja.

“A shirye muke mu taimaka muku wajen buga kudadenku. Za mu yi muku hakan a kan farashi mai rangwame matuka,” inji Emefiele.

Ya ce Najeriya na da karfi da kuma ikon buga kudaden kasancewar ta fara buga nata tun shekarun 1960.

Tun da farko, Gwamnan Bankin na Gambiya ya ce kasarsa na fama da karancin takardun kudade kuma tana bukatar ganin yadda za ta rika wadata kanta da takardun tsawon shekara guda, la’akari da tarin basirar da Najeriya ke da ita a fannin tsawon shekaru.

A cewarsa, yanzu haka sun bayar da kwangilar buga musu kudaden a wasu kasashen, amma a shirye suke su kawo wa Najeriya ita ma ta buga musu muddin ta amince za ta yi hakan.

A nata bangaren, Hukumar Kula da Dab’i da Buga Muhimman Takardun Tsaron Kasa ta ce a shirye take ta fara aikin da zarar kasashen biyu sun cimma matsaya a kan haka.