✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya za ta fara gurfanar da masu taimaka wa ta’addanci a gaban kotu – Malami

To sai dai Ministan ya ki amincewa Ya fadi adadin wadannan mutanen da ake tattarawa.

Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya ce Gwamnatin Tarayya ta fara tattara sunayen mutanen da ake zargi da tallafawa ta’addanci a Najeriya da nufin gurfanar da su a gaban kuliya.

Ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a Abuja lokacin da yake amsa tambayoyi daga ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa.

A cewarsa, binciken wanda yanzu haka yake gudana ya fara samar da gamsassun hujjoji domin gurfanar da wadannan fitattun mutanen da kuma kungiyoyi a fadin kasa.

Malami ya ce kamen wasu wadanda ake zargi a ’yan kwanakin nan ya biyo bayan yanke wa wasu ’yan Najeriya hukunci kan taimaka wa ta’addancin a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

“A sakamakon binciken da muka fara, mun gano cewa akwai kwararan hujjoji dake alakanta wasu fitattun ’yan Najeriya da dama da tallafawa harkar ta’addanci da kudade, kuma muna nan muna tattara sunayensu domin gurfanarwa a gaban kotu,” inji shi.

To sai dai Ministan ya ki amincewa Ya fadi adadin wadannan mutanen da ake tattarawa.