✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Najeriya za ta karbi rigakafin COVID-19 miliyan 4’

Ana sa ran nan da mako mai zuwa za a fara yi wa mutane allurar.

Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta kasa (NPHCDA) ta ce a ranar Lahadi Najeriya za ta karbi allurar rigakafin cutar COVID-19 samfurin Moderna kimanin miliyan hudu.

Babban Daraktan hukumar, Dokta Faisal Shu’aib ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na NTA.

A cewarsa, “Nan da ranar Lahadi, Najeriya za ta karbi rigakafin samfurin Moderna har miliyan hudu, kuma muna farin cikin cewa wannan wata muhimmiyar dama ce ta kara karfafa yakin da muke yi da cutar, musamman sabuwar nau’in Delta da ta sake bulla,” inji shi.

Ya ce Gwamnatin Tarayya ta jima tana sauraron isowar alluran, yana mai cewa Kwamitin Shugaban Kasa kan yaki da cutar tuni ya sami amincewar sayo sabbin na’urorin adana alluran har guda 60, duk da cewa a lokacin babu tabbacin ko nau’in Moderna ko na Pfizer za ta karba.

Dokta Faisal ya ce tuni aka fara karkafa wadannan na’urorin a fadin kasa don ganin an ajiye su a irin yanayin da ya fi dacewa da su.

Ya ce su na sa ran nan da mako mai kamawa za a fara yi wa mutane allurar.