✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya za ta sayi rigakafin COVID-19 miliyan 120 —Fayemi

A cikin shekara biyu za a sayo rigakafin COVID-19 miliyan 120 domin jama'ar Najeriya

Najeriya na shirin sayo rigakafin cutar COVID-19 guda miliyan 120 a cikin shekara biyu domin ’yan kasarta a cikin shekara biyu.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti ya ce kasar za ta sayo allurar rigakafin COVID-19 miliyan 80 a 2021 domin kashi 40 na ’yan kasar, sannan ta karo guda  miliyan 60 a 2022.

Fayemi ya ce gwamnoni na aiki kafada-da-kafada da Gwamantin Tarayya domin tabbatar da ganin rigakafin cutar ta wadata a Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a jawabinsa ga taron Chatham House da ke birnin London na kasar Birtaniya, mai taken ‘Rawar da gwamnatocin jihohin Najeriya za su taka domin farfadowa: Daukar mataki kan kalubalen COVID-19.’

Fayemi ya ce  maimakon matakin gaggawa da Najeriya take dauka a yaki da cutar, tilas ne gwamnoni su mayar da hankali kan inganta bangaren lafiya a Naejeriya.

“Na ba wa gwamnoni kwarin gwiwa su inganta tsare-tsaren jihohinsu na adana da jigilar alluran rigakafi sannan su bunkasa hanyoyin sadarwa da kuma tsarin samar da ita ga masu bukata da sauransu.

“Ta bangaren tattalin arziki kuma babban aikinmu shi ne kare rayuwa. Dole a yi gyara a tsarin kudade na kasa ta yadda kudaden shigan iyalai za su bunkasa.

“Tare muke aiki tare da Gwamnatin Tarayya wajen bullo da shirye-shiryen samar da ayyuka da a halin yanzu ake aiwatarwa,” inji shi.