✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nakasassun ‘yan mata sun koka kan rashin samun mazan aure

A wasu lokutan ma har gatsari ake masu da cewa shin su ma suna lissafa kansu cikin mata ne.

Nakasassun mata a Najeriya sun koka kan yadda maza ke kin neman aurensu har ma da kuma yadda wasu mazan ke nuna masu kyama saboda nakasar da Allah ya dora masu.

Sun bayyana yadda suke shan wahalar samun mazajen aure a duk lokacin da suka isa aure da yadda ake barinsu su rika rayuwa cikin kadaici ba tare da samun abokin rayuwa ba.

Shugabar Hadaddiyar Kungiyar Nakasassu ta Kasa ce ta bayyana haka a wani taron bikin Ranar Mata ta Duniya da aka shirya a Jihar Edo.

 A jawabin da ta yi a wajen taron kamar yadda Jaridar Leadership ta wallafa, ta ce yanzu babban kalubalen da mata nakasassu ke fuskanta shi ne matsalar rashin samun mazajen aure a kasar nan baya ga matsalar kyama da wariya da ake nuna masu a makarantu da wuraren ayyuka.

Ta ce ” babbar matsalar da mata nakasassu ke fuskanta shi ne matsalar wariya ta bangaren aure da ake nuna masu, ta inda maza hatta nakasassun mazan ke kin nemansu da aure.”

Ta kara da cewa “a wasu lokutan ma har gatsari ake masu da cewa shin su ma suna lissafa kansu cikin sahun mata ne.”

A karshe ta yi kira ga jama’a da su tausaya su rika auren mata masu wannan larura saboda irin halin a tausaya masu da suke shiga.