✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nan da karshen 2022 Najeriya za ta fara sarrafa rigakafin COVID-19 – NAFDAC

Ta ce tuni kasar ta cika dukkan sharudan da WHO ta gindaya mata.

Shugabar Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ce Najeriya na dab da fara sarrafa rigakafin COVID-19 a cikin gida.

Ta ce kasar na kokarin ganin ta samar da rigakafin kafin karshen watan Disamban 2022, bayan ta cika sharudan da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta gindaya mata.

Ta bayyana hakan ne yayin jawabin Kwamitin Shugaban Kasa kan yaki da cutar ta COVID-19 a Abuja ranar Litinin.

Shugabar ta NAFDAC ta ce tuni Najeriya ta tsallake mataki na uku kuma na karshe, wanda shi ne zai ba ta damar sarrafa allurar.

Ta ce tun a shekara ta 2018 ne kasar ta fara hankoron ganin ta cimma wannan burin, kuma tuni ta cika dukkan bukata 868 da WHO din ta ba ta, kafin ta amince mata fara sarrafa alluran.

“Ya zuwa 15 ga watan Oktoban 2021, babu wani bukata da Najeriya ba ta cimma ba, yanzu haka kasar tana dab da fara sarrafa rigakafin da kanta,” inji ta.

Ta ce daga cikin bukatar da ake da ita ta dakunan gwaje-gwaje, tuni NAFDAC ta fadada dakin gwaje-gwajen nata da ke Yaba, yayin da yanzu kuma ake kan aikin gina wajen sarrafa rigakafin a Oshodi, dukkansu a Jihar Legas.