✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nan da kwana 2 za mu soke dokar takaita cire kudi idan… —Majalisa

A karo na biyu Emefiele ya ki hallara baan sammacin da Majalisar Tarayya ta yi masa

Majalisar Wakilai ta ba wa Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, wa’adin kwana biyu ya bayyana a gabanta, ko kuma ta dakatar da sabuwar dokar bankin ta takaita cire tsabar kudi.

Shugaban Marasa Rinjaye, Ndudi Elumelu, ne ya bayyana haka a lokacin zaman Majalisar ranar Talata, bayan a karo na biyu Emefiele bai hallara a gabansu.

A makon jiya ne Majalisar ta dage zamanta da Emefiele daga ranar Alhamis zuwa Talata na wannan makon, bayan ta gayyace shi domin tattaunawa kan sabuwar dokar CBN ta takaita cirar tsabar kudi da ta tayar da kura a Najeriya.

Amma a ranar Talata, majalisar ta samu wasika daga Mataimakin Gwamnan CBN Kan Hulda da Jama’a, CBN, Edward Adamu, cewa gwamnan bankin ba zai samu zuwa ba saboda bai dawo Najeriya ba daga wani aiki da Shgaban Kasa Muhammadu Buhari ya tura shi kasar Amurka.

Bayan haka ne, Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila, ya ce Majalisar tana neman cikakken bayani kan irin aikin da zai sa gwamnan bankin zama a kasar waje na tsawon mako biyu.

Ko a makon jiya da Majalisar ta dage zaman zuwa ranar Talata, Mataimakin Shugaban Majalisar, Ahmed Wase, wanda ya karanta wasikar da CBN ta aiko, ya ce Gbajabiamila ya matsar da ranar bayyanar Emefiele ne saboda wani aiki da Shugaba Buhari ya tura shi kasar Amurka.

Shugaban Marasa Rinjayen Majalisar, Ndudi Elumelu, ya ce idan har Gwamnan CBN  din  ya sake ya ki bayyana gabansu a ranar Alhamis, ba gudu ba ja da baya kan kudurinsu na dakatar da dokar.