✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nan gaba kadan za a sako Daliban Kagara —Gumi

Malamin ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da shugabannin ’yan bindigar Neja

Sheikh Ahmad Abubakar Gumi mai yawon yi wa ’yan bindiga wa’azi su tuba ya ce nan da ’yan kwanaki za a sako daliban da aka yi awon gaba da su a makarantar sakandare da ke garin Kagara a Jihar Neja.

Majiyarmu ta ce malamin ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da shugabannin ’yan bindiga Fulani a Dajin Dutsen Magaji ranar Alhamis, bayan da aka sace mutanen su 42 daga makarantar a daren Laraba.

Majiyar ta tabbatar wa Aminiya cewa daliban tare da wasu matafiya da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su na nan lafiya kuma an kusa sako su ga iyalansu.

Ta ce Gwamnatin Jihar Neja ta amince ta yi sulhu da ’yan bindigar kuma ta tura tawagarta don tattaunawa.

Shugabannin ’yan bindigar sun kai Sheikh Gumi wani kauyen Fulani da suke zargin sojoji sun kona, suka yi masa luguden bama-bamai tare da jefa gawarwakin mutane a cikin rijiyoyi.

Don haka suka sun soki matsayin Gwamna El-Rufai na Jihar Kaduna na kin sulhu ko biyan diyya ga Fulani.

Tuni dai malamin da tawagarsa suka isa garin Minna, hedikwatar Jihar Neja da misalin karfe 3 na Asubahin Juma’a daga ziyarar da suka kai Dajin Dutsen Magaji bayan kwashe kusan sa’a bakwai a kan hanya.

Tun da farko wata majiya ta bayyana cewa daya daga cikin shugabannin kungiyoyin ’yan bindigar, Dogo Gide ya ce a shirye suke su sako duk mutanen da ke hannunsu da zarar an biya musu bukatunsu.

Dogo Gide ya bayyana hakan ne a ganawarsu da malamin a dajin da ke Tegina a Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja.

Sai dai ta ce Dogo Gide bai kai ga bayyana bukatun nasu ba ga Sheikh Gumi.

Ta ce malamin ya dauki matakin ba da gudunmawa ne don kashin kansa na tattaunawa da shugabannin masu garkuwa da mutane game da muhimmancin  zaman lafiya.

A yayin da yake nasiha, Sheikh Ahmad Gumi, ya kuma bayyana musu muhimmancin zaman lafiya daga mahangar Musulunci a lokacin ganawar tasu.