✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nan gaba maza za su rasa matan da za su aura —Bincike

Bincike ya ce akwai yiwuwar nan gaba kashi biyu cikin uku na maza za su rasa matan aure.

Wani bincike kan alkaluman jinsi a duniya ya gano cewa wasu matakai da mutane ke dauka a kan haihuwa za su kawo karancin mata a duniya a nan gaba.

Rahoton binciken da cibiyar lafiya ta BMJ Global Health ta gudanar kan bambancin tsakanin jinshi, ya nuna son haihuwar ’ya’ya maza da kuma al’adar kyamar haihuwar mata sun sa ana yawan zubar da cikin ’ya’ya mata ko kashe jarirai mata a wasu kasashe.

Binciken da cibiyar ta gudanar a kasashen 204 ya nuna daga shekarar 1979 zuwa 2017 an kashe jarirai mata ko an zubar da cikinsu sau miliyan 45.

Sakamakon binciken ya ce a shekarar 1970 da ’yan kai, jararai maza da aka haifa a Kudancin Turai da Asiya sun fi mata, kasashen Indiya da Pakistan kuma ke da kashi na 95 cikin 100 na jarirai mata da aka zubar da cikinsu ko ake kashewa.

Marbucin rahoton, Dokta Fengqing Chao, ya ce a halin yanzu, maza na fama da karancin matan da za su aura a wasu daga cikin kasashen da abin ya shafa.

Rahoton ya ce Najeriya da Pakistan na daga cikin kasashen da nan gaba maza za su iya fin mata yawa, amma abin zai yi sauki bayan shekara 20 masu zuwa.

Dokta Chao ya ce daga yanzu zuwa shekarar 2030 akwai yiwurar rasa jarirai mata 4.7 kuma illar ta wuce batun rashin samun matar aure.

Ya ci gaba da cewa idan ba a yi wa tufkar hanci ba, nan gaba a cikin kowandanne maza uku, mutum daya ne zai matar da zai aura.

Don haka, “Akwai bukatar yin dokoki da za su tabbatar da daidaiton jinsi domin magance karancin abokan arue,” inji.

Ya ce: “Karancin mata a cikin al’umma na iya haifar da miyagun dabi’u da tashin hankali da kuma kawo cikas a zamantakewar al’umma.”