✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAPTIP ta ceto mutum 11 da aka yi fataucinsu

Hukumar ta ceto mutum 11 da aka yi yunkurin ketarawa da su zuwa Libya da Italiya.

Hukumar Hana Fataucin Mutane ta Kasa (NAPTIP) ta ceto mutum 11 da ake zargi yin safarar su tare da cafke wadanda ake zargi da sato su.

Shugaban hukumar NAPTIP reshen Jihar Kano, Abdullahi Babale ne, ya bayyana haka a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a ranar Alhamis.

Ya ce an dauko wadanda aka ceto ne daga jihohin Kogi, Ekiti, Edo da kuma Ebonyi.

A cewarsa, “An yi safarar su zuwa Libya, Italiya da Dubai, don yin karuwanci da kuma aikatau.”

Ya kara da cewa hadin gwiwar ’yan sanda tare da jami’an hukumar ne suka kama mutanen 12 a kan iyakar Babban Mutum a Jihar Katsina.

Bugu da kari, Babale ya bayyana cewa wadanda aka yi safarar tasu ’yan shekara 17 zuwa 36 ne, sai kuma mai shekaru 41 a cikinsu, wanda ake zargi da yin safarar su.

Babale ya jaddada cewa hukumar tana gudanar da bincike kuma za ta gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.