✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nasarorin da Maradona ya samu a kwallon kafa

Maradona ya shahara a musamman harkar kwallon kafa a duniya.

Shararren tsohon dan wasan kwallon kafar Argentina, Diego Armando Maradona ya cimma nasarori da dama a rayuwarsa ta kwallo kafin rasuwarsa a ranar Laraba.

Maradona ya rasu ne bayan ya sha fama da ciwon zuciya; an sallame shi daga asibiti bayan an masa aiki a kwakwalwarsa.

Maradona ya lashe gasar cin Kofin Duniya da kasarsa ta Argentina a 1986, inda ya zura kwallo 2 a wasan da suka buga da Ingila.

Ya buga wa Argentina wasa daga 1976 zuwa 1981 kuma ya buga wasanni 167, yayin da ya jefa kwallo 115.

Diego Maradona

Kungiyoyin da ya taka Leda

  • Ya taka leda a kungiyar Boca Junior daga 1981 zuwa 1982, inda ya buga wasanni 40 kuma ya ci kwallo 28.
  • A Barcelona, ya yi wasa daga 1982 zuwa 1984, ya buga wasanni 36 ya kuma zura kwallo 22.
  • A kunungiyar Napoli ya taka leda daga 1984 zuwa 1991, ya yi wasanni 188, kuma ya jefa kwallo 81.
  • Ya buga wasanni 26 a Sevilla daga 1992 zuwa 1994 kuma ya ci kwallo 5.
  • A kungiyar Newell’s Old Boys daga 1993 zuwa 1994 ya buga wasanni 7 ba tare da ya zura kwallo ko daya ba.
  • Daga nan ya sake komawa Boca Junior a 1995 zuwa 1997, ya buga wasanni 30, ya jefa kwallo 7.
  • Baki daya a tarihin rayuwarsa ya buga wasanni 494, ya jefa kwallo 258.

 

  • Gasar da ya lashe
  1. A shekarar 1981 Maradona ya lashe gasar Argentinean Championship na kasar Argentina
  2. A 1982 ya lashe gasar Spanish League Cup da kungiyar Barcelona
  3. A 1983 ya lashe gasar Spanish Super Cup da Barcelona
  4. A 1986 ya lashe gasar cin Kofin Duniya da kasarsa ta Argentina
  5. A 1987 ya lashe gasar Italian Cup da kungiyar Napoli
  6. A 1989 ya lashe gasar UEFA-CUP da Napoli
  7. A 1990 ya lashe gasar Italian Championship da Napoli
  8. A 1991 ya sake lashe gasar Italian Super Cup da Napoli

 

  • Kyaututtukan da ya lashe
  1. Maradona ya lashe kyautar Gwarzon Dan Wasa na Kudancin Amurka (South American Footballer of the year) a 1979, 1986, 1989, 1990 da 1992.
  2. Gwarzon Dan Wasan Kukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA player of the century) a 1986.
  3. Kyautar kwallo mafi kyau a gasar cin Kofin Duniya na 1986.
Diego Armando Maradona

Kungiyoyin da ya horar

  • Maradona ya horar da kungiyar Textil Mandiyu a 1994
  • Daga nan ya karbi ragamar horar da Racing Club a 1995
  • Ya horar da kungiyar kwallon kafa ta Argentina daga 2008 zuwa 2010
  • Bayan shafe wasu shekaru ba tare da shiga harkokin wasanni ba, a 2011 ya karbi aikin horar da kungiyar Al-Wasl kuma ya ajiye aiki a 2012
  • A 2013 zuwa 2017 ya karbi aikin mataimakin mai horar da kungiyar Deportivo Riestra
  • Daga 2017 zuwa 2018 ya karbi kungiyar Fujairah domin horar da ita
  • 2018 zuwa 2019 ya horar da Dorados de Sinaloa.
  • Sai 2019 zuwa 2020, inda ya karbi horar da kungiyar Gimnasia de La Plata.

Masu harkar wasanni a fadin duniya suna jinjina irin hidima da rawar da marigayi Maradona ya taka a fagen harkar wasanni, musamman kwallon kafa.