✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NATO ta fara shirin atisaye da dakaru dubu 30 a Norway

NATO ta fara shirin atasaye da dakaru dubu 30.

Dakarun Kungiyar Tsaron Kawance ta NATO sun fara gudanar da wani gagarumin atisayen soji a kasar Norway.

Atisayen wanda aka yi wa take ‘Cold Response’, dakaru dubu 30 ne za su gudanar da shi daga kasashe 23.

Jiragen yakin sama kimanin 200 da kuma jiragen yakin ruwa 50 na cikin atisayen sojojin na kasashen kungiyar tsaro ta NATO, wanda zai kai har zuwa ranar 1 ga Afrilu kafin a kammala shi.

Matakin ya zo ne a daidai lokacin da duniya ta shiga zaman dar-dar sakamakon yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine.

Lamarin na zuwa ne a yayin da Rasha ke ci gaba da kai hare-hare a sassan kasar, domin hana makwabciyar tata kasancewa mamba a NATO, da a yanzu ta kaddamar da atisayen soji.

A karshen makon da ya gabata dai Rasha ta tsananta hare-haren da take kai wa cikin Ukraine, wannan karo a bangaren Arewaci da kuma Yammacin kasar.

A halin yanzu alkalumma na cewa mutane 35 sun rasa rayukansu a daya daga cikin hare-haren jiragen yakin da suka kai barikin Lviv kusa da iyakar Ukraine da Poland.