✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NATO ta yi zaman sasanci kan rikicin Ukraine da Rasha

Kasashen biyu sun dauki tsawon lokaci suna musayar yawu, wanda kowane ke cikin shirin ko ta kwana.

Kasar Amurka da wasu kasashen Tarayyar Turai sun gudanar da taro a hedikwatar kungiyar tsaro ta NATO a wani shiri na kawo karshen rikicin Ukraine da Rasha.

Sau uku ana tsara yin zaman kan rikicin kasashen biyu, amma wannan shi ne karo na biyu da aka yi zaman.

Akalla dakarun Rasha dubu 100 ne yanzu haka ke kan iyakar kasar da Ukraine, a cikin cikin shirin ko-ta-kwana a dai-dai lokacin da ake fargabar yiwuwar Rasha na iya mamaye Ukraine din baki daya.

Sai dai bayan zaman tattaunawar Amurka da Rasha ciki har da ganawar tawagoginsu a Geneva a ranar Litinin, Moscow ta sanar da yiwuwar iya samun jituwa.

Tattaunawar wakilan bangarorin hudu da aka gudanar a hedikwatar NATO da ke birnin Brussels a ranar Laraba, ta mayar da hankali wajen ganin an shawo kan rikicin kasashen biyu ta fuskar maslaha maimakon daukar matakin soji.

Rasha na sake nanata batun ganin cewa lallai NATO ba ta ba wa Ukraine damar zama mamba a cikinta ba, a yayin da Amurka ke cewa kungiyar da mambobinta ke da hurumin sahale wa Ukraine zama mamba ko akasin haka ba wai wata kasa ba.