✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nau’ukan tsuntsayen da ke aman wuta yayin farauta

Ana samun tsuntsayen ne a yankin Arewacin kasar Australia.

A kasar Australia, an gano wasu tsuntsaye da ke tayar da wutar da ke haddasa gobarar daji ta hanyar sarrafa wuta domin farautar abincin da za su ci.

Tsuntsayen dai na yin aman wuta tare da sarrafa ta wajen samun abincinsu.

Wadannan tsuntsaye da ake kira da “firehawks” a turancin Ingilishi ana samun su ne a yankin Arewacin kasar ta Australia.

Daga cikin tsuntsayen masu tayar da wuta akwai wanda ake kira da black kite (Milvus migrans), whistling kite (Haliastur sphenurus), da kuma brown falcon (Falco berigora) da ma wasu wadanda ba a ambata ba.

Mutanen yankin sun gano cewa wadannan tsuntsayen na iya sarrafa wutar ta hanyar daukar itace mai ci da wuta da bakinsu ko faratansu zuwa wasu wuraren bayan sun tayar da wutar.

An kara gano cewa tsuntsayen kan tayar wuta ne a matsayin tarko domin ta koro kwari da dabbobin da ke labe a  wuraren da suka sanya wutar.

Da zarar wurin ya fara ci da wuta, kwarin da dabbobin suka fito domin tsira, sai tsuntsayen su rika bi suna kalaci da su.

Idan kuma aka yi rashin sa’a ba su samu yadda suke so ba, sai su kara daukar wani tsinke mai wuta zuwa wani wuri su kara yin irin hakan.

A wani bincike da aka tattara a baya-bayan nan wanda aka buga a mujallar Journal of Ethnobiology, an gano cewa yawan gobarar daji da ke samu a yankunan da wadannan tsuntsaye ke rayuwa na da nasaba da wannan dabi’a ta tsuntsayen.

Duk da cewar daya daga cikin marubutan rahoton binciken, Mark Bonta, da ke aiki da Hukumar Yanayi ta kasar da kuma masanin yanayin kasa a Jami’ar Jihar Penn, na ganin cewa binciken da suka yi ba zai wadatar ba wajen tabbatar da  haka, bisa la’akari da cewa sama da shekaru 40,000 tsuntsayen na rayuwa a yankunan.

Sai dai har yanzu ba samu tabbacin dalilin da ya sa wadannan tsuntsaye ke tayar da wutar ba, wasu na ganin da gangan ne wasu kuma na ganin cewa suna tayar da wutar ne yayin da suke farautar abinci.