✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nazari da tambihin kalaman kyautata rayuwa (4)

Jama’a masu karatu, assalamu alaikum. Yau ma  kamar yadda muka faro mako uku da suka gabata, za mu ci gaba ne da nazari da tambihin…

Jama’a masu karatu, assalamu alaikum. Yau ma  kamar yadda muka faro mako uku da suka gabata, za mu ci gaba ne da nazari da tambihin wasu kalaman kyautata rayuwa da muka ci karo da su a wurare daban-daban. Kamar yadda bayani ya gabata, irin wadannan kalamai na hikima, magabata ne masu fasaha da hikima da basira suka furta su, mu kuma za mu ci gaba da amfana da su, kasancewar hikima kayan al’umma ce. Allah Ya albarkace mu da dacewa da tasirin kowace hikima, amin.

Kalamin farko da za mu tattauna a kansa a yau, ya fito ne daga bakin wani magabacin mai hikima, wanda ba mu tantance sunansa ba, amma dai ga abin da yake cewa: “Gara ka yi shiru kada a san kai wawa ne, da ka buda bakinka ka tona wa kanka asiri.”

Lallai kam, wannan bayani ya fassara kansa da kansa, kodayake bari mu bi kadinsa domin tsintar darasin da ke kunshe a cikinsa. Kamar yadda al’amura suke gudana, mafi yawan jama’a ba su san cewa magana na da kima da tasiri ba a rayuwa. Abin da ya kamata mu gane shi ne, ita magana wata irin abu ce mai siffa, wacce ke bayyana halaye da kamannin mai yin ta. Idan mutum mai hikima ne da basira da hankali, ta hanyar maganganun da yake yi jama’a za su gane haka. Haka kuma, idan mutum wawa ne, dolo, marar tsinkaya da ilimi, duk dai ta hanyar maganganunsa za a fahimta da haka. Don haka, mu kasance muna kula da abubuwan da muke furtawa na magana, mu rika yin maganganun da suka dace da halayenmu na kwarai, domin kuwa da su ne za a auna mutuncinmu da kamalarmu. Ya fi sauki da fa’ida ga mutum ya kame bakinsa ya yi shiru, maimakon ya ce zai saki baki yana maganar da ba ta da amfani ga rayuwarsa da kuma rayuwar sauran al’umma da ke kusa da shi. Kada kuma mu manta da karin maganar nan ta Hausawa, wacce ke cewa, magana zarar bunu ce, idan ta fita ba ta komawa. Kamar dai yadda wani mawaki ya ce ne, “Malam iya bakinka, in ka kiya ya ja maka…” Haka dai batun yake, domin kuwa bakinka dai shi ne linzaminka.

Yanzu kuma sai mu shiga batu na gaba da muka zakulo muku, watau inda wani mai hikima shi ma ya ce: “Ingancin rayuwar mutum daidai yake da dagewarsa a kan kyawawan sakamako, koma mece ce sana’arsa ko aikinsa.”

Babbar magana, wai dan sanda ya ga gawar soja! Kamar yadda rayuwa take, kowane mutum yana son ya ga cewa ya samu ci gaba, ya samu gamsassar nasara a rayuwarsa. Idan aikin gwamnati ko na kamfani mutum yake yi a rayuwarsa, yana matukar bukatar ya ga cewa ya samu nasara, ya samu ci gaba ta fuskar karin girma da sauransu. Idan kuma wata sana’a yake yi ta kashin kansa, babu shakka yana son ya ga cewa ya samu nasarar ci gaba, yana son ya ga sana’ar tasa ta habaka, ya samu riba mai yawa, ta yadda zai fadada sana’ar tasa. To, abin tambaya a nan shi ne, ta yaya mutum zai samu nasara da ci gaba a aikinsa ko sana’arsa da yake yi? Duk da cewa akwai abubuwa da yawa da mutum zai yi domin samun irin wannan gamsassar nasara da ci gaba, amma babban ginshikin da mutum zai sanya gaba shi ne dagewa da jajircewa.

Dagewa ko nacewa da maida hankali kacokan ga aikin da mutum ke yi ko sana’a, su ne za su zama linzaman da za su jagorance shi zuwa ga nasara. Duk abin da mutum zai yi, yana bukatar maida hankali da nacewa da dagewa da jajircewa. Dole ne mutum ya maida hankali, duk abin da mutum zai yi ya nuna cewa da gaske yake yi, ba tare da wasa ko kasala da kasawa ko kosawa ba. Wannan jajircewa ita ce ke gadar ko samar da sakamako mai kyau da cin nasara ga abin da aka tunkari aikatawa. Misali, ko noma kake yi a gona, muddin ba ka dage ka maida hankali da nacewa ba, cikin lokaci gonar taka za ta zama saura, ciyawa ta kucce maka. Idan haka ta faru kuwa, amfaninka ba zai yi nagarta ba, wanda haka zai sanya ka yi asarar noman, maimakon ka samu nasara. Amma idan kullum kana yin abin da ya dace, kuma a lokacin da ya dace, babu shakka za ka ci gajiyar karin maganar nan da ke cewa, bawan damina, tajirin rani.