✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NBC ta datse gidan rediyon Biafra daga watsa shirye-shirye a Legas

Hukumar Dake Kula da Kafafen Watsa Labarai ta Kasa (NBC) ta datse gidan rediyon nan na Biafra daga ci gaba da watsa shirye-shiryensa a sassa…

Hukumar Dake Kula da Kafafen Watsa Labarai ta Kasa (NBC) ta datse gidan rediyon nan na Biafra daga ci gaba da watsa shirye-shiryensa a sassa da dama na jihar Legas.

Gidan rediyon dai wanda ke aiki ba bisa ka’ida ba ya jima yana yada labarun karya, shirye-shiryen kin jinin kasa da kuma yunkurin tayar da zaune tsaye.

Sai dai NBC  a cikin wata sanarwa ta ce ta datse gidan rediyon ne daga ci gaba da watsa shirye-shirye la’akari da tanade-tanaden kundi na 11 na dokokin Najeriya na 2004 wanda ya hana kowanne mutum ko wata kungiya daga watsa shirye-shirye ba tare da samun lasisi daga gwamnati ba.

A cewar sanarwar, tuni aka umarci dakarun Rundunar Tsaron Farin Kaya (DSS) da na Rundunar ’Yan Sanda ta Kasa da su cafko wadanda ke da hannu wajen tafiyar da haramtaccen gidan rediyon.

“Sadara ta biyu, sashe na biyu na dokokin da suka kafa NBC ya bayyana karara cewa babu wanda zai yi amfani da kowacce irin na’ura domin watsa kowanne irin sakon murya ko bidiyo ta hanyar rediyo, talabijin, satilayit, ko kuma kowacce irin hanya ta watsa labarai daga kowanne sashe na Najeriya sai da amincewar tanade-tanaden wannan kudirin doka,” inji sanarwar.

Gidan rediyon dai wanda Kungiyar ’Yan Awaren Biafra na IPOB, karkashin Nnamdi Kanu ke gudanarwa ya jima yana watsa shirye-shirye daga wurin da har yanzu ba a kai ga gano ina ne ba, ba tare da samun izini daga hukumar ta NBC ba.