✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NCAA ta dakatar kamfanin da jirginsa ya lalace yana shawagi

Hakan na zuwa ne bayan kamfanin jirage da ya fi jimawa a Najeriya ya dakatar da ayyukansa

Hukumar Sufurin Jiragen Aama ta Najeriya (NCAA) ta dakatar da kamfanin jirgagen sama na Dana Air na wucin gadi daga ranar Laraba 20 ga watan Yuli, 2022.

Babban Daraktan Hukumar, Kyaftin Musa Nuhu ya bayyana cewa an NCAA ta dauki matakin dakatarwar ne bayan Dana Air ya karya dokar gudanar da kamfanin jirgi da kuma ta gudanar da kamafanonin jirage masu zaman kansu ta Najeriya.

Umarnin dakatarwar da Kyaftin din ya sanya wa hanunu dai tuni ta isa ga Hukumar gudanarwar kamfanin jirgin Dana Air.

Sanarwar dakatarwar da Babban Daraktan na NCAA ya fitar, ta bayyana cewa an yi hakan ne bayan sakamako binciken kundin matsalolin tattalin arziki da Hukumar ta yi wa kamfanin.

Sai kuma binciken sirri da ta gudanar kan ayyukansa na baya-bayan nan, inda aka gano kamfanin ba shi da wadataccen kudin da zai iya ci gaba da gudanar da aiki ma inganci.

Idan ba a manta ba dai a ranar Talata ne wani jirgin mallakin Dana Air ya yi saukar gaggawa a Abuja, bayan injinsa ya lalace a lokacin da yake tsaka da shawagi a sararin samaniya.

Wannan dai na zuwa ne rana guda da kamfanin jirgin da ya jima yana jigila a NAjeriya wato Aero ya dakatar da gudanar da aikinsa.