✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NCC ta hana a caji masu amfani da waya kudin USSD

Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), ta umarci kamfanonin sadarwar su daina cajar mutane kudaden sakonnin tes da ake turo masu daga banki ko wata kafar…

Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), ta umarci kamfanonin sadarwar su daina cajar mutane kudaden sakonnin tes da ake turo masu daga banki ko wata kafar kasuwanci ko in sun nemi wani bayani (USSD).

Hukumar ta ce, bai kamata a caji masu amfani da wayoyin sadarwar kudin da bankuna da kamfanoin sadarwar ke karbar ba.

Mukaddashin Shugaban NCC, Umar Danbatta, a wata sanarwar ya ce an yin hakan ne don kare hakki da kyautata wa ‘yan Najeriya, tare da samar da cigaba a fannin sadarwa.

“Hukumar NCC ta dauke wa kwastomomi biyan kudaden, ta kuma umarci bankuna da kamfanonin sadarwar tare da ba su damar yin maslaha kan hanyar da za su bi ta sa farashin da kowannensu zai karu”, inji Danbatta.

Ya ce an yi hakan ne saboda rikicin da aka dade ana yi tsakanin kamfanonin sadarwar da bankuna kan wa zai sauke cajin da ake yi wa masu amfani da wayoyin hannun, ko kuma ya farashin zai kasance.

“Mun san cewa tsare-tsaren da muke yi suna bukatar sauyi daga lokaci zuwa lokaci, hakan kuma ya ta’allaka ne da yadda dama ta bayar” kamar yadda ya kara bayyanawa.

Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, ya ba da umurnin samar da sabon farashin USSD da ake cajar kowanne bangare sakamakon tsarin biyan USSD da NCC ta bijiro da shi.