✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

NDDC: Majalisa ta ba Akpabio awa 48 ya fadi masu karbar kwangila

Idan bai fadi sunayen wadanda suka karbi kwangilar ba, za mu kai shi gidan yari.

Majalisar Wakilai ta ba wa Ministan Neja Delta Godswill Akpabio wa’adin sa’a 48 ya fallasa ‘yan Majalisar da suka karbi kwangiloli a Hukumar Kula da Yankin na Neja Delta.

Majalisar ta yi barazanar kai Akpabio gidan yari idan bai bayyana sunayen ‘yan majalisar da ya zarga da karbar kwangiloli a NDDC ba.

Akpbio ya yi zargin ne a ranar Litinin, lokacin da yake amsa tambayoyi a gaban Kwamitin Majlisar kan NDDC da ke binciken zargin ruf da ciki a kan Naira biliyan 81.5 a hukumar.

Ya ce ‘yan majalisar sun karbi kwangiloli daga hukumar ta NDDC da ke karkashin ma’aikatarsa.

Wa’adin da Majalisar ya zo ne a lokacin zaman babban zaurenta na ranar Talata, bayan Shugaban Masu Rinjaye, Ndudi Elumelu ya samu goyon bayan takwarorinsa wajen kalubalantar zargin ministan da ya kawo hujjar zargin da ya yi.