✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta cafke dan bindiga mai shekara 90

Tsohon an cafke shi yana shirin safarar miyagun kwayoyi ga ’yan bindiga.

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ta cafke wani tsohon soja mai shekara 90, kuma rikakken dan bindiga.

An kama tsohon mai suna Adamu ne a Mailalle, Sabon Birni, a Jihar Sokkwato, bisa laifin safarar makamai da kwayoyi ga ’yan bindiga.

Kakakin NDLEA na kasa, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Abuja.

Babafemi ya ce wanda ake zargin yana dauke da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 5.1 a lokacin da aka cafke shi.

Ya kara da cewa an kama wani matashi dan shekara 37 dan asalin Jihar Edo da laifin safarar miyagun kwayoyi.

Babafemi ya ce an kama matashin ne ne da kulli 41 na tabar wiwi a Filin Jirgin Sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

Ya kara da cewa, wanda ake zargin, wanda tuni aka tsare shi, yana shirin shiga jirgin Turkish Airline zuwa birnin Milan na kasar Italiya, ta birnin Santanbul na kasar Turkiyya a ranar 30 ga watan Yuli.