✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NDLEA ta fitar da sunayen sabbin ma’aikatan da za ta dauka

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ce ta fitar da sunayen wadanda suka sami nasarar samun guraben aiki da ita.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ce ta fitar da sunayen wadanda suka yi nasarar samun guraben aiki da ita.

Kakakin hukumar, DCN Jonah Achemah, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Juma’a.

Mista Jonah ya shawarci wadanda suka yi nasarar da su ziyarci shafin hukumar a kan www.ndlea.gov.org domin duba sunayensu, yana mai cewa tuni aka aike wa wadanda abin ya shafa sakonni ta imel da kuma rubutaccen sako.

A cewarsa, an dauki sabbin ma’akatan ne a matakai daban-daban, bayan an gayyaci wasu daga cikinsu wata jarrabawa.

‘Ma’aikata 5,000 muka dauka’

Ya ce, “Sabbin ma’aikatan, wadanda adadinsu ya kai 5,000, za su hallara a Makarantar Horar da Jami’an NDLEA da ke Rikkos a birnin Jos na jihar Filato domin tantancewa daga ranar 10 zuwa 23 ga watan Janairun 2021 da misalin karfe 9:00 na safe.

“An rarraba su zuwa rukunai hudu yayin tantancewar saboda a tabbatar da kiyaye matakan kariya daga COVID-19.

“Ana bukatar kowanne sabon ma’aikacin da ya hallara akalla kwana daya kafin ranar da aka tsara domin tantance shi,” inji Mista Jonah.

‘Za su karbi takardun daukar aikinsu bayan tantancewar’

Ya kara da cewa a yayin tantancewar ne za a ba kowannensu takardar daukar aiki kuma za su fara aiki da zarar an kammala tantance su.

“Saboda haka, ana bukatar sabbin ma’aikatan su zo da takardar shaidar asibiti dake nuna matsayin lafiyarsu, da takardunsu na karatu na ainihi da kuma kwafinsu, da takardar haihuwa da kuma ta yankin da suka fito.

“Ana kuma bukatar su zo da takardar shaidar lafiya daga amintaccen asibitin gwamnati, gajerun wanduna guda biyu, riga da kuma takalmin kanbas,” inji kakakin na NDLEA.

A watan Yulin 2019 ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince a dauki ma’aikatan su 5,000 domin inganta ayyukan hukumar.

An dai fara shirye-shiryen daukar su ne a watan Agustan 2019, yayin da aka gudanar da jarrabawar a watan Disambar 2019 da Janairun 2020.